Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Fashin Daji Sun Kashe Jami’an Sa Kai Kimanin 30 A Jihar Neja


‘Yan Fashin Daji
‘Yan Fashin Daji

Kimanin jami’an tsaron sa kai 30 suka mutu a wani kazamin arangama da suka tafka da ‘yan fashin daji a jihar Nejan Nigeria.

NIGER, NIGERIA - Bayanai daga yankin Dogon Dawa ta karamar Hukumar Mariga a jihar suna cewa, a karshen makon nan da ya gabata jami’an tsaron sa kai sun yi wani yunkurin aukawa ‘yan fashin dajin to amma sai ‘yan fashin suka yima ‘yan sa kan kwanton bauna.

Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunanshi ya ce gwabzawar da akayi tsakanin barayin da wadannan jami’an tsaron na sa kai suma dai ‘yan fashin dajin da dama sun rasa rayukkansu.

Shugaban karamar hukumar ta Mariga Hon. Abbas Kasuwar Garba ya tabbatar da aukuwar lamarin ya kuma nemi jama’a da su kwantar da hankali, yayinda gwamnati ke gudanar da bincike akan wannan tashin hankali da ya faru.

Kawo lokacin hada wannan rahoto babu wani karin haske daga rundunar ‘yan sanda ta jihar Neja akan lamarin.

Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:

‘Yan Fashin Daji Sun Kashe Jami’an Sa Kai Kimanin 30 A Jihar Neja.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG