Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Adamawa Ta Bukaci Taimakon Gwamnatin Tarayya


Kofar shiga garin Mubi a Jihar Adamawa a bayan da aka kori 'yan Boko Haram daga cikin garin
Kofar shiga garin Mubi a Jihar Adamawa a bayan da aka kori 'yan Boko Haram daga cikin garin

Kamar dai yadda alkalumma ke bayyanawa fiye da gadoji biyar ne mayakan Boko Haram suka lalata a arewacin jihar Adamawa,wato kama daga na Maiha har zuwa na yankin Madagali, da Micika .

Kuma ana cikin yadda za’a gyara gadojin ne sai ga wata sabon targade na rugujewar gadan Michika wanda
shi ya hada kananan hukumomin Michika da Madagali,kuma rugujewar wannan gada yanzu ya maida hannun agogo baya a yunurin da hukumomi da kuma kungiyoyin agaji na kasa da kasa ke yi na tallafawa al’ummomin da suka koma yankunan su a wannan yankin.
Gwamnatin jihar dai tace aikin yafi karfin ta wanda adon haka nema ta mika kokon baranta ga gwamnatin tarayya data kai dauki.
Da yake zantawa da manema labarai gwamnan jihar Adamawan
Sen.Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla ya bukaci gwamnatin tarayya ne data taimaka. Yana mai fadin cewa

‘’Mu dinnan gwamnoni mun gana da shugaba Muhammadu Buhari ance za azo a fara aiki mu damuwar mu gadojin mu hanyoyin mu, har yanzu kaga abinda ya faru da gada a can Minchika da wasu wuraren ma gadojin suna yankewa ne mu kuma gwamnatin jihar bamu da kudin da zamu yi wadannan ayyukan, aikin gadoji dama hakki ne na gwamnatin tarayya su zo suyi wannan aikinta har yanzu muna jira mu gani a gyara wannan hanyoyin kana a gyara gadajen nan

To ko me wakilan wadannan al’ummomi ke yi ne ayanzu? Wannan itace tambayar da wakili sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz yiwa yar majalisar dattawa Sen.Binta Masi Garba dake wakiltar Adamawa ta arewa a majalisar dattawa.?

Ga Ibrahim Abdulazeez da Karin bayani 2”49

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG