Daya cikin jigajigan Jamiyyar APC a Najeriya kuma dan Majalisar dattawa mai wakiltan Jihar Borno ta Kudu, Sanata Mohammed Ali Ndume ya yi kira ga Shugaba Mohammadu Buhari da ya yi koyi da Shugaban Amurka Joe Biden a bangaren yi wa kasa jawabi akai-akai musamman kan abin da ya shafi tsaron kasa.
Kusan mako guda kenan da kai wa makarantar horar da sojoji ta kaduna- NDA hari, amma har yanzu Shugaba Mohammadu Buhari bai fito ya yi wa kasa jawabi ba.
“Duk abin da ya faru nan ya kamata ya fito ya yi magana, ko daga dakin kwanansa ya yi magana da ‘yan Najeriya, wannan yana da muhimmanci. Ga abin da yake faruwa a Afghanistan, kullum sai shugaban Amurka ya yi magana” In ji Ndume wanda shi ne shugaban Kwamitin kula da harkokin sojin kasa a Majalisar Dattawa.
Sanatan na magana ne kwanaki bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai makarantar horar da sojoji ta NDA da ke Kaduna inda suka kashe sojoji biyu suka yi garkuwa da daya.
Sai dai ji kadan bayan harin fadar gwamnatin kasar ta Najeriya ta fitar da sanarwa ga ‘yan Najeriya inda ta yi ikirarin cewa harin zai karawa dakarun kasar kaimin yaki da ta’addanci.
“Wannan danyen aiki zai zaburar da dakarunmu wajen kawar da duk wasu muggan ayyuka, wanda sojojinmu suka kuduri aniyar aiwatarwa nan ba da jimawa ba.” Adesina y ace.
“Buhari ya sha alwashin cewa mutuwar dakarun ba za ta tafi a banza ba, domin za a dauki matakin da zai mayar da martanin da zai kawar da baragurbin da ke kasar.” Adesina ya kara da cewa.
Sai dai a ganin Sanata Ndume, ya fi kyau a ji daga bakin shugaba Buhari maimakon a ji a wani waje.
“Ya fi a ji daga bakinsa maimakon a ji daga bakin Ndume ko wani dan amshin shata.”
Ndume ya ce Buhari ya ce lokaci ya yi da Buhari zai mike ya karbi ragamar mulkin kasar domin shi ne Shugaban Kasa, ba masu magana da yawunsa ba.
Mai magana da yawun gamaiyar kungiyoyin Arewa CNG, Abdulazeez Suleiman ya fito fili karara ya ce akwai abin dubawa a yadda Shugaban Kasa Mohammadu Buhari yake kin yin bayani a wannan yanayi na tabarbarewar harkar tsaro a kasar.
“Kullum sai a ce an ci kafinsu, amma a ce har suna da karfin da za su shiga wuri irin NDA, su shiga gidaje biyar su kashe sojoji su dauke babban hafsan soja su tafi har yanzu ba labari, a ce shugaba bai taso ya zo NDA nan ba.” In ji Suleiman.
Sai dai Kwararre a fanin kundin tsarin mulkin kasa Barista Mainasara Umar, ya ce shugaban kasa yana da hurumin sauke hadimansa da ba sa aiki yadda ya kamata, hakazalika, yana da hurumin sauya shugabanin hukumomin tsaron kasar da Ministocinsa in bai gamsu da aikinsu ba Domin shi ne shugaban kasa mai cikakken Iko.
Mai magana da yawun Dakarun Sojin Najeriya, Manjo Janar Benjamin Olufemi Sawyer ya fitar da sanarwa cewa za su ci gaba da gudanar da ayyukansu don gano duk wanda ke da hannu cikin wannan danyen aiki.
Saurari rahoto cikin sauti daga Medina Dauda:
Akwai Darussa Da Kasashe Za Su Koya A Rikicin Afghanistan Bayan Janyewar Amurka - Diop