Wannan na zuwa ne lokacin da wannan mummunan dabi'a ke ci gaba da wanzuwa a cikin al'umma, a sassa daban daban na kasar.
Gwamnatin Najeriya na ci gaba da fafutukar yaki da dabi'ar sha da safarar miyagun kwayoyi da wasu sanadarai masu sa maye, sai dai kuma masu wannan harkar na ci gaba da aika-aikar su.
Alal misali a jihar Sakkwato kacal dake arewa maso yammacin Najeriya, daga watan daya na wannan shekara zuwa yanzu, hukmar NDLEA ta kama kayan maye masu nauyin kilo gram 812.258kg a hannun mutane 86 da ta kama, a cewar Kwamandan ta a jihar, Iro Adamu Muhammad.
A wani yunkuri na salon kawar da wadannan munanan dabi'u hukumar ke tunatar da masu wurare da ake amfani da su wurin aikata munanan auyukan cewa su shiga taitayinsu, domin idan ba su daina ba za su yi asarar wuraren komin girmansu, kamar yadda Kwamanda Iro Adamu ya ja kunne akai.
Wani abu da hukumar ke nuna takaici akai kuma shi ne yadda wannan matsalar ta kutsa har gidajen matan aure.
Masu lura da lamuran yau da kullun na ganin cewa yaki da sha da fataucin kwayoyi da kayan maye dai abu ne da ke bukatar kulawar gaske kafin a iya kawar da shi a cikin al'umma, don haka akwai bukatar shigowar kowa wajen samun nasara akai.
Mai fafatuka akan wannan matsalar Nuradeen Abdullahi Attajiri na ganin gwamnati ma ya kamata ta kara karfafa jami'anta dake wannan fama.
Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:
Dandalin Mu Tattauna