An yi bitar halin da tsaron kasar ke ciki a taron wanda ya gudana karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma daukacin manyan hafsoshin sojin kasar baki daya.
Babban hafsan hafsoshin rundunan sojojin ruwan Najeriya, Vice Admiral Ibok -Ite Ikwe Ibas ya yiwa ‘yan jaridu karin bayani jim kadan bayan kammala taron.
“Ya ce a makwanni biyu kawai da suka gabata Boko Haram sun kai hare hare kimanin 27 a shiyar arewa maso gabashin Najeriya kadai, amma jaruman dakarun mu sun dakile hare haren har ma sun hallaka kwamandodin masu tada kayar bayar”.
Taron majalisar tsaron Najeriyan kazalika ya kuma cimma shawarar fara janye sojoji daga wasu yankunan arewa maso gabashin Najeriya a shekarar 2020 mai kamawa.
Sai dai wasu a cikin dattawan arewa maso gabashin Najeriyar ir sun bayyana fargaban janye sojoji daga wannan shiya.
Ga cikakken rahoton daga Hassan Maina Kaina daga Abuja:
Facebook Forum