Cikin 'yan kwanakin nan dai mayakan Boko Haram sun shiga kai sabbin hare hare a wasu yankuna na jihohin Adamawa, Borno da kuma Yobe, wadanda su ne lamarin yafi shafa.
Kuma na bayan nan shi ne yunkurin da su ka yi na shiga garuruwan Biyu, da kauyukan Gombi da kuma Madagali da ke kusa da dajin Sambisa, wanda ke zama tungar 'yan bindiga masu tada kayar bayan.
To sai dai kuma yayin da mayakan Boko Haram ke kaddamar da sabbin hare hare, rundunar sojin Najeriya na sauya lale, domin magance wannan matsalar inda babban hafsan sojin kasar Laftana Janar Yusuf Tukur Burutai shi da wasu kusoshin soji su ka ziyarci jihar Adamawa, domin ganin halin da ake ciki.
Janar Burutai wanda ya soma yada zango a hedikwatar rundunar soji ta 23 dake Yola don kaddamar da asibiti, da kuma masaukin baki kafin ya wuce Madagali, ya yaba da nasarorin da ake samu yanzu.
Ya ce wadannan nasarori abin yabawa ne kuma rundunar sojin zata ci gaba da kare diyaucin Najeriya da kuma gudanar da ayyukan jinkai a cewar babban hafsan sojin Najeriya din.
Mallam Yakubu Musa, wani manazarci kan harkokin da ke faruwa a rikicin Boko Haram, ya gaya mana ta bakinsa, inda ya ce mayakan Boko Haram na cigaba da kai hare haren ne saboda a san su na nan.
Ga rahoto cikin sauti.
Facebook Forum