Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Iya Shawo Kan Boko Haram Idan Aka Magance Cin Hanci Da Rashawa A Najeriya


Sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka John Kerry, ya fada yayin ziyarar da ya kaiwa mai martaba sarkin Musulmi a Najeriya cewa, za a iya shawo kan kungiyar Boko Haram idan gwamnatocin suka magance cin hanci da rashawa da kuma samar da dama ga matasa.

Ziyarar ta uku wadda kuma mai yiwuwa ita ce ta karshe da Kerry zai kai a Najariya a matsayinsa na sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka, tazo ne a daidai lokacin da kasar ke fama da barazanar komadar tattalin arziki da kuma matsalolin tsaro dabam dabam.

Da yake jawabi a fadar mai martaba Sarkin Musulmi Sa’adu Abubakar, Kerry yace, hakin gwamnati ne ba al’umma damar da zata hana su shiga kungiyoyin ta’addanci.

Yace, idan ana so a cimma masalaha da kyakkyawar makoma, tilas ne kasashe ba kawai zasu yi kokarin kawo karshen tsaurin ra’ayin dake goyon bayan ‘yan ta’adda kadai ba, amma tilas su samarwa al’ummarsu wata damar da tafi waccan. Kerry yace, babu wani abin ban haushi da takaici da karya guiwa da ya shige, al’ummar kasa su yi tunanin, gwamnati ta cuce su.

Ya kushewa kungiyar Boko Haram da ta kashe sama da mutane dubu ishirin tare kuma sanadin rasa matsugunan sama da mutane miliyan biyu da dubu dari biyar cikin sama da shekaru bakwai da kungiyar ke kokarin kafa shari’ar Islama.

Kerry ya alakanta yaki da kungiyoyi kamar Boko Haram da yunkurin shekara da shekaru na yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, da masu kula da lamura suka ce ya yi sanadin talauta galibin al’ummar kasar miliyan dari da saba’in.

Shugaba Muhammadu Buhari ya lashe zabe bara bisa alkawarin yaki da cin hanci da rashawa da kuma sauya yadda ake gudanar da ayyukan gwamnati a kasar da ta kasance daya daga cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika.

Shugaba Muhammadu Buhari ya jadada matsayinsa na yaki da cin hanci da rashawa a ganawarsa da Kerry a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.
Yace, zamu sake horas da ma’aikatanmu yadda zasu fahimci inda muka sa gaba. Wadanda kuma suka sabawa doka, za a hukumtasu komi matsayinsu.

Yayinda wadansu masu kula da lamura suke korafin cewa, gwamnatin ta saba alkawarin yakin neman zaben da tayi, Kerry yace Amurka tana goyon bayan yunkurin yaki da cin hanci da rashawa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG