Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomin Kano A Nuwamba


Wata dattijiya take kada a kuri'arta.
Wata dattijiya take kada a kuri'arta.

Hukumar zaben jihar Kano mai zaman kanta (KANSIEC) ta sanar da cewa za ta gudanar da zabubbukan kananan hukumomi a ranar 30 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Shugaban Hukumar Zaben ta KANSIEC, Sani Lawal Malumfashi ne ya bayyana hakan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Kano a yau Laraba.

Malumfashi ya kuma zayyana jadawalin yadda zaben zai gudana.

A cewarsa, za a fitar da sanarwa game da zaben a ranar 15 ga watan Nuwambar. Za a samar da takardun takara tun daga 1 ga Oktoba har izuwa 11 ga watan, inda za a kammala mayarda takardun a ranar 18 ga watan Oktoba mai zuwa.”

Ya kara da cewa za a tantance ‘yan takara da ga 18 zuwa 20 ga watan Oktoban, bayan hakan za a fito da sunayen sahihan ‘yan takara a ranar 24 ga watan Oktoba mai zuwa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG