Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Taliban Ta Gargadi Jama'a Kan Zaben Afghanistan


.Wani hari da kungiyar NATO ta kai Afghanistan
.Wani hari da kungiyar NATO ta kai Afghanistan

Kungiyar mayakan Taliban ta ce sam, sam ba sauran wata maganar sulhu tsakaninta da gwamnatin kasar Afghanistan, sannan kuma ta nemi mutanen kasar, wadanda suka gaji da yakin da kasar ta jima tana fuskanta, da cewa su gujewa zaben ‘yan majalisar wakilai na kasar mai zuwa, wanda Taliban tace “sojan mamaye da Amurka ke shugabanta” ne suka shirya shi.

Sanarwar da ‘yan Taliban din suka bada ta biyo ne bayan tayin da shugaban kasar Afghanistan Asharaf Ghani yayi ne a ranar Assabar da ta wuce, inda ya sake neman kungiyar Taliban da cewa ta fito ta shiga zaben na ran 20 ga watan Oktobar wannan shekara, a matsayin jam’iyyar siyasa.

Wannan tayin na shugaba Ghani, wanda tun cikin watan Fabrairu yayi shi, ya sami yabawa sosai daga ciki da wajen kasar ta Afghanistan.

Sai dai ‘yan Taliban na ci gaba da yin watsi da tayin a bisa hujjar cewa har yanzu “Afghanistan na karkashin mamayen dubban sojojin kasashen waje wadanda duk wasu kudurorin siyasa da na soja su ne suke yanke shawara a kansu.”

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG