Bayan da wani dan harin kunar bakin wake ya halaka mutane 57 ya kuma raunana wasu fiyeda da dari a birnin Kabul, hukumar zaben Afghanistan mai zaman kanta tana fargabar cewa rashin tsaro zai karya wa mutane guiwar fitowa domin zaben 'yan majalisa dana kananan hukumomi.
Kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai harin a jiya Lahadi, a wata cibiyar rarraba katin sheda, inda daruruwan mutane suka hallara domin su nemi katin saboda zaben kasar mai zuwa.
Mukaddashin shugaban hukumar zaben kasar Maazullah Dawlati, yace rashin tsaro zai kashe guiwar masu kada kuri'a, lamari da zai kassara tsarin na tafarkin demokuradiyya.
Facebook Forum