Inda suka tabbatar da cewa wannan kasuwa zata ci gaba da kasancewa a rufe, don sun gano cewa akwai kanshin gaskiya cikin rade radin da akeyi na cewa ana shigo da dabbobin sata zuwa wannan Kasuwa.
Fiye da kwanaki 20 ne hukumomin sojan Najeriya suka bada sanarwar rufe kasuwar, hade ma da wasu kasuwannin a jihar Yobe, wanda tun a wancan lokacin ne aka ringa samun korafi daga jama’a da dama, musammam masu sana’a a kasuwannin da Mayanka.
Sai dai gwamnati tace har yanzu akwai bukatar karin hakuri don sun gano cewa wannan zargi da ake na kawo Shanun sata kasuwar da mayanka akwai kanshin gaskiya cikin ta. Don kuwa ana son a sami zaman lafiya ne mai daurewa, kuma wannan hanyar na daya daga cikin hanyoyin da yan Boko Haram ke samun kudi don ci gaba da ta’addancin su.
Shugaban kungiyar matasa masu aikin sa kai na Civilian JTF, Mallam Jafar Lawan, ya tabbatar da cewa wannan zargi haka yake, kuma akwai bukatar yan kasuwar su kara hakuri.
Domin karin bayani.