Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zimbabwe Ta Fi Fuskantar Hadarin Matsalar Tsutsa Mai Cinye Amfanin Gona - FAO


Robert Mugabe,Shugaban Zimbabawe
Robert Mugabe,Shugaban Zimbabawe

Hukumar samar da abinci da noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa, kasar Zimbabwe za ta fi kowacce kasa a kudancin Afrika fama da tsutsar dake cinye amfanin gona.

Bincike na nuni da cewa, yankunan Gokwe da Zhombe dake yankin Midlands na kasar ne matsalar za ta fi shafa.

Hukumar samar da abinci ta FAO tace mai yuwuwa tsutsar ta lalata sama da kadada 130 na gonakii a kasar ta Zimbawe.

Ita wannan tsutsar tafi barna a gonakin masara, abinda kasar Zimbabwe tafi nomawa.

Hakan ne kuma ya haifar da fargaba ainun a kasar dake fama da karanci abinci.

Kasar Zimbabwe na daya daga cikin kasashen da suka fuskanci matsalar fari shekarun 2005 da 2006 sakamakon matsalar El-Nino da aka fuskanta a lokacin damina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG