Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babbar Kotun Tarayya Ta Sallami Karar da Aka Yiwa Ibrahim Geidam


Alhaji Ibrahim Geidam, gwmamnan Yobe
Alhaji Ibrahim Geidam, gwmamnan Yobe

Babbar kotun tarayya ta sallami karar da aka shigar akan gwamnan Yobe Ibrahim Geidam

Karar akan lamura uku ne da suka hada da daukan rantsuwa fiye da sau biyu a matsayin gwamna da zargin yin anfani da takardar karatu ta bogi da kuma fitar da shi Mustapha Dan Mai Hajja karfi da yaji daga tsayawa takara.

Hukuncin ya biyo bayan korar wata karar magudin zabe da dan takarar PDP Adamu Maina Waziri ya shigar.

Daya daga cikin wadanda suka yi takara a karkashin APC Injiniya Mustapha Dan Mai Hajja ne ya shigar da karar da neman a cire gwamna Ibrahin Geidam daga mulki.

Bukar Mustapha Gonori kwamishanan shari'a na jihar Yobe ya nuna gamsuwa da hukuncin kotun. Yace daga hukuncin mai bin sawu shi ya zama barawo. Shi dake zargin ba'a yi wasu abubuwa ba kotu tace shi ne bai cika wasu ka'idodi ba.

Yace iyayen jihar sun yi masa magana ya janye karar amma ya ki. Gonori yace jiha ce da ta yi fama da rikice-rikice. Yanza take farfadowa saboda haka kamata yayi duk 'yan jihar su hada hannu jihar ta yi gaba.

Hukuncin bai yiwa mukarraban Mai Hajja da lauyoyinsa dadi ba domin sun lashi takobin daukaka kara tare da cigaba da karar har zuwa kotun koli in ta kama hakan.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG