Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jama'atul Nasril Islam Tana Zargin Rufa-Rufa Kan Badakalar Sayo Makamai da Jirgin Shugaban CAN


People wear Samsung Gear VR devices as they attend the launching ceremony of the new Samsung S7 and S7 edge smartphones during the Mobile World Congress in Barcelona, Spain, Feb. 21, 2016.
People wear Samsung Gear VR devices as they attend the launching ceremony of the new Samsung S7 and S7 edge smartphones during the Mobile World Congress in Barcelona, Spain, Feb. 21, 2016.

Babban sakataren kungiyar jama'atul Nasril Islam Dr. Khalid Abubakar Aliyu ne yayi wannan zargin a wani taron manema labarai a Kaduna.

Da yake magana a taron manema labaran, Dr. Khalid, yace kungiyar ta kira taron ne domin ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na magana kan abun ashsha, da aika aika-aika game da kama jirgin shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya da wasu mutane a Afirka da kudade masu yawan gaske wai sun tafi sayo makamai.

Babban sakataren yace abun mamaki a gunsu shine da gwamnatin tarayya ta fito tace ai da saninta aka yi wannan shirin sayo makaman.

Dr. Khalid yace lallai lallai suna da yakini, cewa akwai hannun boye da yake shigan burtu a hare haren da ake kaiwa da sunan ta'addanci a Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Shiga Kai Tsaye

Daga nan yaci gaba da yin tambayoyi wai shin ina mutanen da ake kamawa da zargin shiga ayyukan ta'adanci a wurare daban daban a Najeriya, ina aka kaisu, an yi musu hukunci kuma a ina?

Wakilin Sashen Hausa a Kaduna Isah Lawal Ikara ne ya halarci taron manema labaran kuma ya aiko bayanin.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG