Amurka da wasu kasashen larabawa sun kai hari da jiragen yaki kan kunigiyar ISIS a Syria.
Kakakin ma’aikatar tsaron Amurka da ake kira Pentagon leftanar kanal Jeff Pool ya gayawa Muryar Amurka cikin daren nan anan Amurka cewa an kai hare haren ne da jiragen yaki, da kuma jiragen yaki na ruwa wadanda suka harba makamai masu linzami. Duk da haka yace saboda ganin ana ci gaba da kai wadannan hare hare ba zai bada Karin bayani ba.
Leftanar Kanal Pool bai bayyana kasashen larabawa da suke cikin jerin kasashe da suke kai hare haren ba, amma wani jami’in Amurka wanda bai so a bayyana sunansa ba yace kasashen sun hada da Bahrain, da Saudi Arabia, da Jordan da hadaddiyar daular larabawa.
Shugaban Amurka Barack Obama da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry cikin makonni da suka wuce suna matsin lamba kan kasashen duniya su shiga sahun rundunar taron dangi kan kungiyar ISIS.
Ahalinda ake ciki kuma, mayakan kurdawa suna ci gaba da kare wani gari da yake kan iyaka daga harin mayakan kungiyar ISIS, a dai dai lokacinda yawan ‘yan gudun hijira daga yankin da suke shiga Turkiya ya haura dubu 130.