Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gudun Zaman Kashe Wando Ya Sanya Ni Shiga Harkar Fina-Finai – inji Adam A Zango


Adam A Zango
Adam A Zango

Filin duniyar Fina Finai na wannan makon ya samu bakoncin bako na musammam, wato jarumi Adam A Zango wanda akafi sani da suna Yarima, wanda ya bayyana mana cewa rashin aikin yi ne ya shigar dashi masana’antar fina finai bayan da ya kammala karatun sa.

Yarima dai yace bayan gama karatunsa na sakandare ne yayi tunanin maimakon ya zauna (zauna gari banza), sai yaga ga sana’ar da ta dace da shi kuma zai iya yinta kasancewar yayi wasanni da kade-kade da raye-raye a makaranta. Tun dai shekara ta 2001 wato shekaru goma sha uku kenan da suka wuce Adam A Zango ya fara aikin yin fina finai.

Alokacin da Adam yazo masana’antar hada fim ya fara koyar kida a dalilin rashin samun shiga fim, inda ya fara koyar kida a gurin Ibrahim Danko har ya kware, hakan ne yasa ake ta neman sa domin yayi waka Allah kuma ya bude masa domin duk wakar yayi sai ta karbu.

Daga baya bayan ya rasa wanda zai saka shi a fim sai Adam A Zango, ya fara tara kudin sa da niyyar yim fim dinsa na kansa, ya kuma nemi abokansa dake yin sana’ar har suka nemo labari da darakta da jarumai aka biya su suka fara aikin fim din har ya kammala, fim din mai suna “Sirfani” shine fim din san a farko.

Bayan fitowar “Sirfani” ne wasu daga cikin masana’antar ne kamar su Ali Nuhu da Naja CSB Jakara da Bauni suka gano cewa lallai wannan zai iya cin abinci a wannan harka, daga nan dai suka fara saka shi cikin wasannin su Allah kuma ya daukaka shi. Cikin fina finan da yayi “Ahalil Kitabi” itace ya kira bakandamiyar sa.

Saurari cikakkiyar hirar Yarima wato Adam A Zango.

XS
SM
MD
LG