‘Yan sanda a arewacin Najeriya, sun ce sun ceto yara (maza), da maza (manya) sama da 300 da aka tsare a wata makarantar Islamiyya inda da yawansu an sha yi ma su duka an kuma keta haddinsu.
‘Yan sandan sun fadi cewa galibin mutanen da aka ceto, daure da sarka aka same su a lokacin da jami’an tsaro suka kai wani samame a birnin Kaduna ranar Alhamis bayan da aka kwarmata masu bayanin abinda ke faruwa.
Wata kafar talabijin ta nuna yadda yawancin mazan da yaran ke cikin mawuyacin hali, duk sun galabaice kuma da kyar su ke tafiya.
Makarantar na daukar dalibai ne don ta koya ma su karatun Alkur’ani ta kuma taimaka wajen sauya tunanin wadanda suke shan miyagun kwayoyi ko kangararru. Ko da yake, ‘yan sanda sun ce makarantar ba ma ta da izinin koyar da wani abu kwata-kwata.
Rundunar ‘yan sandan ta ce an kama mai makarantar da wasu malamai su 6 a samamen da aka kai.
Facebook Forum