Shugaban kungiyar, Olumide Akintayo, ya fada cewa a wasu kasashen duniyar kamar Amurka, ana gudanar da kashi 80 cikin 100 na ayyukan yin rigakafi ne a kantuna ko wuraren sayar da magunguna dake unguwanni ko gundumomi. Yace kwararrun likitocin magunguna, sune jama'a suke fara tuntuba idan su na da wata matsalar rashin lafiya.
Mr. Akintayo yace "Kashi 40 cikin 100 na dukkan yaran dake mutuwa su na kanana, ko matan dake mutuwa lokacin haihuwa a duk fadin duniya, ana samunsu ne a kasashe biyu tak a duniyar, a Najeriya da kuma Indiya. Menene dalilin haka? Saboda gwamnati a kasashen biyu tana yin ko oho da kwararrun likitocin harhada magunguna da wasu ma'aikatan lafiyar dake da kwarewar da zata iya taimakawa wajen rage wadannan mace-mace."
Yace a yanzu, "nan da mako uku zaka ji labarin cewa an samu sabbin yara guda uku da suka kamu da kwayar cutar Polio a nan Najeriya."