Ayau talata 10/7/2018 za'a dawo fagen fafatawa a gasar cin kofin duniya 2018 wanda yake gudana a kasar Rasha, a matakin wasan dab da na karshe, (Semi final) tsakanin kasar Faransa da Belgium da misalin karfe bakwai na yammanci agogon Najeriya Nijar Kamaru da kasar Chadi.
Bisa tarihin haduwa wasa tsakanin kasashen biyu France da Belgium tun daga 1992 zuwa 2015 an kara sau 8 France ta samu nasara sau 3 ita kuma Belgium sau 2 anyi kunnen doki sau 3, Kuma duk a wasanin sada zumunci tsakanin kasa da kasa ne.
A shekara ta 1992 an tashi 3-3 sai kuma 1996 Faransa ta doke Belgium 2-0 sai 1998 Faransa ta samu nasara 1-0 a shekara ta 2002 kuwa kasar Belgium ce ta doke Faransa da kwallo 2-1.
An buga canjaras babu ci a 2011 da 2013 sai kuma haduwarsu ta karshe 2015 inda Belgium, ta samu nasara akan Faransa da kwallaye 4-3, Sai kuma wannan haduwar wadda ba a san maci towoba sai miya ta kare.
Facebook Forum