Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Najeriya Ta Cika Shekaru 55 da Samun 'Yanci daga Birtaniya


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Sheakaru 55 da suka gabata Najeriya ta samu 'yancin kai daga turawan mulkin malka na Birtaniya

A daren 30 ga watan Satumbar shekarar 1960 aka kada taken Birtaniya na karshe.

Da misalin karfe goma sha biyun dare wato daya ga watan Oktoba aka kada taken Najeriya a karon farko wanda ya nuna didimar samun 'yancin kai.

A ranar 15 ga watan Janairun 1966 wasu hafsoshin sojojin Najeriya suka kaddamar da juyin mulki na farko inda shugabanni irinsu Sir Ahmadu Bello, Alhaji Abubakar Tafawa Balewa, Birigedia Mai Malari, Chief Samuel Akintota da wasu manyan sojoji daga arewacin Najeriya suka rasa rayukansu.

Manjo Janar Joseph Aguyi Ironsi ne ya dage kan karagar mulkin kasar amma watanni shida da wasu 'yan kwanaki yayi yana mulki saboda wasu sojojin sun hambarar dashi ranar 29 ga watan Yulin 1966.

Janar Yakubu Gowon shi ya karbi mulkin kasar daga Ironsi wanda ya rasa ransa a wannan juyin mulkin yayinda sojoji suka sameshi a Ibadan inda ya kai ziyara. Sun kasheshi tare da mai masaukinsa Kanal Adekunle Fajuyi.

A shekarar 1967 Janar Gowon ya kirkiro jihohi 12 daga yankuna hudu na kasar abun da gwamnan yakin gabashin kasar Kanal Ojukwu ya ki amincewa dashi. Daga bisani ya mayarda yankin kasa mai 'yancin kai wadda ya kira Biafra. Wannan abun da Ojukwu ya yi shi ya janyowa kasar yakin basasa na tsawon shekaru uku.

Bayan yakin basasa da Janar Gowon ya ki shirya zabe ya mayar da kasar tafarkin dimokradiya Janar Murtala Muhammad ya hambarar dashi. To saidai shi ma din bai dade ba domin wani yunkurin juyin mulki na ranar 13 ga watan Fabrairun 1975 da bai yi nasara ba ya dauku ransa.

Janar Olusegun Obasanjo ya gaji Murtala Muhammad shi ne kuma ya mayar da kasar hannun mulkin farar hula a shekarar 1979 lokacin da Alhaji Shehu Shagari ya zama shugaban kasa..

Gwamnatin Shagari bata kare wa'adi na biyu ba da sojoji suka hambarar da ita. Janar Muhammad Buhari ya zama shugaban kasa. Amma a shekarar 1985 Janar Ibrahim Babangida ya kwace gwamnati daga hannun Buhari.

Janar Babangida ya shirya zabe a shekarar 1992 wanda Chief M. K. Abiola ya kama hanyar lashewa amma sojoji suka yi masa katsalandan suka soke zaben.

Janar Babangida ya fuskanci matsi saboda soke zaben lamarin da ya sa ya mika milki ga Chief Earnest Shonekan a shekarar 1993. Shi ma watanni shida ya yi da Janar Sani Abacha ya kawar dashi daga mulki.

Ranar 8 ga watan Yuni na shekarar 1998 Allah ya karbi ran Janar Abacha. Janar Abdulsalami Abubakar ne ya maye gurbinsa.

A shekarar 1999 Janar Abubakar ya mayarda kasar kan mulkin dimokradiya inda Janar Olusegun Obasanjo mai murabus ya dare karagar mulki a matsayin shugaban kasa na farar hula.

Bayan Janar Obasanjo ya yi wa'adi biyu Alhaji Musa 'YarAddu'a ya gajeshi. Da Allah ya yi masa rasuwa mataimakinsa Dr Goodluck Jonathan ya cigaba da mulki. Ya tsaya zabe sau daya ya lashe a shekarar 2011. Amma bai samu nasara ba a zaben 2015 saboda Janar Muhammad Buhari shi ya ci ya kuma karbi mulkin kasar.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG