Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Amurka Za Ta Dauki Mataki Kan Ayyukan Soji a Iran


Kakaki Majalisar Wakilan Amurka Pelosi
Kakaki Majalisar Wakilan Amurka Pelosi

Kakakin Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi, ta sanar a jiya Laraba cewa Majalisar za ta kada kuri’a a yau Alhamis da za ta tursasawa shugaba Donald Trump ya gaggauta kawo karshen ayyukan soji akan Iran.

Kudurin zai bukaci sai shugaban kasa ya yi cikakken bayani ga Majalisun kasar kafin ya dauki wani matakin soji, lamarin da ya bude wata sabuwar mahawara a kan ikon shugaban kasa kan daukar matakin soji.

Pelosi ta fitar da wata sanarwa mai cewa, a matsayin mu na ‘yan Majalisa mun samu kwanciyar hankali, bayan da shugaba Trump ya ce zai janye daga rikicin soji da kasar Iran. Amma ‘yan Majalisa na bangaren Democrat suna tababa a kan batun kai harin jirgi mara matuki a makon da ya gabata da ya kashe Manjo Janar Qassim Suleimani, haka kuma basu gamsu da bayanin tawagar Trump ta bayar na kai harin ba, tare da yin alkawarin daukar mataki a kan ikon da shugaban kasa ke da shi na shiga yaki.

‘Yan Democrat sun ce kuri’ar ta yau Alhamis, za ta hada da matakin da zai bukaci shugaba Trump ya tsagaita wuta a kan ayyukansa na soji a kan Iran har sai Majalisun kasar sun kada kuri’ar amincewa. Wannan mataki ka iya fuskantar kalubale a Majalisar Dattawa mai rinjayen 'yan Republican, amma a jiya Laraba, wasu ‘yan Republican biyu sun bayyana aniyarsu na marawa natakin baya. Ko ta wace hanya, wannan batu zai haifar da zazzafar muhawara a kan manufar Trump a kan Iran da kuma rawar da Majalisar Dokokin za ta taka wurin takawa shugaban kasar burki game da shiga yaki.

Pelosi ta fada a sanawarta cewa ‘yan Majalisun Dokokin kasar suna da matukar damuwa mai bukatar matakin gaggawa nan gaba, a kan shawarar gwamnati na shiga yaki da Iran da kuma rashin dabarunta. “Bamu samu maganin damuwar mu a cikin kudurin ikon shiga yaki da shugaban kasar ya gabatar da kuma bayanin da gwamnati tayi a jiya”, inji Plosi.

Aminu Yakubu Lame mai fashin baki ne a kan harkokin yau da kullum, ya yi tsokaci a kan kai ruwa rana da ake yi tsakanin fadar White House da Majalisun Dokokin kasar:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:07 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG