Shugaban Amurka Donald Trump ya yiwa Iran barazanar kai mummunar hari a kan cibiyar al’adun Shi’a idan ta maida martani akan harin da ya kashe babban jami’in sojanta Qassem Soleiman, a makon da ya gabata.
"Su dai a ganin su an amince su kashe mutanen mu, su azabtar da mutanen mu su dasa bama bamai a gefen hanya su hallaka mutanen mu, amma a ce bai yiwuwa mu kai hari a kan cibiyar al’adun Shi’a? hakan ba zai yiwu ba," inji Trump a hirarsa da manema labarai a cikin jirgin Air Force One a daren jiya Lahadi.
Sai dai bai fadi ainihin abubuwan da zai auna ba. Amma masana doka sun ce kai harin bam a kan cibiyar al’adun shi’ar zai zama take dokokin kasa da kasa, haka zalika a sakonsa na Twitter a safiyar jiya Lahadi ya ce Amurka za ta maida martani kan harin Iran, da kai hari mai tsanani.
Shugaban kasar ya fadawa manema labarai cewa yana nazarin fitar da bayanan sirri da suka kai shi ga ba da umarnin kashe Soleimani.
Facebook Forum