Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Juma’a, rana ce da MDD ta ayyana domin ta zama ranar alkinta yanayi a duniya


Shugaban Amurka Barack Obama (File photo)
Shugaban Amurka Barack Obama (File photo)

Miliyoyin al’ummar kasa da kasa na bikin tunawa da ranar alkinta yanayi ta duniya a yau Juma’a ta hanyar daukan alkawarin daddasa itatuwa da furanni tare da inganta hanyar samun iskar shaka mai lafiya.

Bikin wannan rana shine na 41 da za’a yi a Amurka bayan afkuwar bala’in rubzawar rijiyoyin mai a tekun yammacin Amurka da suka gurbata ruwan teku da harkokin noma da kamun kifi har da shi kansa yanayin illahirin yankin ruwan tekun. Yanzu ana gudanar da bikin tunawa da ranar alkinta yanayi a kasashe sama da metaan a duniya. A nan Amurka jami’an dake shirya bikin sun yi kira ga al’ummar kasa da kasa da su taimaka su bada cikakken hadin kan shuka itatuwa da furanni domin samar da iska mai lafiya ga mutane da dabbobi da cikakkiyar lafiyar yanayin zama.

A jawabin da yayi domin fara bikin na alkinta yanayi a Amurka, shugaba Barack Obama ya yaba da karfin halin dukkaan wadanda suka sanaya hannu domin karfafa mutumcin wannan rana tare da jaddada karfin alkawarin da Amurka tayi na shiga sahun gaban kasashen dake alkinta yanayi a duniya kuma yayi fatan Amurka zata ci gaba da rike matsayin ta wajen tinkrar kalubalen da sauye-sauyen yanayi ke haifarwa. Ita ma uwargidan shugaban Amurka Michelle Obama ta shirya bada tata gudmmawar domin bunkasa muhimmancin wannan rana ta alkinta yanayi ta duniya wajen fita zuwa unguwannin talakawa domin tayasu tsaftace muhallinsu da kwashe datti daga kan tituna, koda yake an tsaida ayyukan saboda ruwan saman da ake yi a babban birnin na Amurka Washington D.C.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG