Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi a Afirka Ta Kudu Zasu Dauki Gawar Nelson Mandela Zuwa Qunu Inda Za'a Yi Jana'izarsa


Akwatin Gawar tsohon shugaban Afirka ta kudu Nelson Mandela da aka lullube da tutar kasar.
Akwatin Gawar tsohon shugaban Afirka ta kudu Nelson Mandela da aka lullube da tutar kasar.

Yau Asabar hukumomi a Afirka ta Kudu zasu kai gawar Mr. Nelson Mandela da jirgin sama zuwa garinda aka haifeshi bayanda aka aje gawar a Pretoria na kwanaki

Yau Asabar hukumomi a Afirka ta kudu zasu kai gawar Mr. Nelson Mandela da jirgin sama zuwa garinda aka haifeshi bayanda aka aje gawar a Pretoria na kwanaki, inda dubban masu makoki suka je domin karramawa da kuma yin banwaka da gawar.

Jami’an kasar suka ce kamar mutane dubu dari ne suka ziyarci gawar Mandela yayinda aka a jiyeta a babban dakin taro dake binrin Pretoria da ake kira Union Buildings har na kwanaki uku.

Wani wakilin Muriyar Amurka Peter Cox, yace ‘Yansanda sunyi faman daidaita gungun mutane masu juyayin mutuwar Mandela, wadanda suka kawo ziyara ganin gawar,suka yi kokarin tsallake shingayenda ‘Yansanda suka girka da nufin ganin gawar kamin a kawo karshen wannan damar a wunin jiya. Mutane da yawa ne suka fadi,sakamakon wata ‘yar turereniya da ta auku, kamin a sake maido da oda a wurin.

‘Masu makokin sun shiga layi tun karfe 3 na daren Alhamis domin su sami sukunin shiga zaurenda gawar take.

Daya daga cikin ‘yan makokin Dr. Mulumba yace ba ya son wannan damar ta kubuce masa na ganin Mr. Mandela wanda Allah ya yiwa rasuwa makon jiya yana da shekaru 95 da haifuwa a duniya.
XS
SM
MD
LG