Bayan ga shugabanin kasashe, haka kuma dubban yan jarida daga kasashe zasu halarci abinda ake sa ran zai zama daya daga cikin jana'iza mafi girma a tarihin Afrika ta Kudu.
A yayinda ake ci gaba da yin ta'aziyar mutuwar Mandela, akwai wadanda suka yi doguwar tafiya zuwa birnin Johanesburgh domin mutunta Mandela.
Wani da ya taka da kafa yace Mandela ya taka muhimmiyar rawa sosai wajen hada kawuna bakar fata da jar fata. Yanzu muna iya mu'amala da sauran mutane cikin walwala ba tare da jin tsoron ko za'a kama ka ba.
Wannan wani dalibin kimiyar computa ne wanda yaje da abokansa domin tunawa da wasu daga cikin irin abubuwan da Mandela yayi a rayuwarsa. Tiha Tologo da yan uwanta sunyi tukin kusan kilomita dari hudu da hamsin zuwa tsohon gidan Mandela a Johanesburgh
Tace sun zo ne daga Pamplerstad wani dan karamin gari a arewacin Cape. Tafiyar sa'o' shidda ne. Kuma mun zo ne mu mutunta Tata. Shi Babanmu ne kuma shi kakanmu ne. Shine shugaban Afrika ta kudu na farko bakar fata. Kuma wannan lokaci ne na tarihi, muma kuma son mu zama bangaren wannan tarihi shi yasa muka zo.
Su kuma Christine da Angel Ntanda, basu dade da komawa Johanesburgh da zama ba daga jamhuriyar Congo. Sun tafi da yayanusu guda uku zuwa gidan Mandela domin su ajiye furanin kalo. Shi dai Ntanda wanda yayi aiki da dare, ya yanke shawara mancewa da ya kwanta ya huta a jiya litinin domin ya kai iyalinsa wurin da aka kebe domin tunawa da Mandela
Yace yaje ne domin karama Nelson Mandela. Shi ba tsohon shugaban Afrika ta kudu bane. Muna jin cewa muma shugabanmu ne, domin a saboda shi wani abu ya faru a kasar mu Congo. Ntanda yace Mandela ya taimaka a ka yi shawarwarin kula yarjejeniyar samun zaman lafiya a kasarsu Congo.
Shugabanin kasashen duniya da sauran jama'a zasu ci gaba da tunawa da Madiba dukkan wannan makon. A ranar Lahadi idan Allah ya kaimu za'a yi jana'izarsa a garinsu Qunu.