Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Samu Rigakafin COVID-19 Amma WHO Tana Tattaunawa A Kai


Shugaba Vladmir Putin
Shugaba Vladmir Putin

A jiya Talata Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce tana tattaunawa da Rasha game da sabon rigakafin COVID-19 da aka amince dashi kwanan nan.

A jiya Talatan Rasha ta zama kasa ta farko da ta amince da allurar rigakafin ga dubban 'yan kasarta. A cikin bayyanin da ya yi ta gidan talabijin na Rasha, Shugaba Vladimir Putin ya ce, an tabbabtar da ingancin kuma anyi "dukkanin gwaje-gwajen da ake bukata."

Ya ce an baiwa 'yarsa maganin rigakafin, kuma bayan an yi musu sau biyu, zafin jikin su bai canza ba, “adadin kwayoyin kariya na jikin su ya karu.”

Wannan sanarwar ta zo ne bayan da duniya take cikin matsanancin shakku a saboda rigakafin ta samu karbuwa kasa da watanni biyu na gwaji a Rasha.

Kakakin hukumar WHO a Geneva Tarik Jasarevic ya ce, "Muna tattaunawa da hukumomin kiwon lafiya na Rasha kuma ana ci gaba da tattaunawa game da yiwuwar samar da rigakafin, amma sai an sake kwakkwaran bincike da tantance dukkan bayanan lafiya da ake bukata."

Jasarevic ya ce, yana karfafa gwiwa da saurin yadda za a iya samar da rigakafin a duniya. Ya ce babban abin da ke damun hukumar ta WHO shi ne ta iya rarraba rigakafin a duniya.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG