An fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isira’ila da kungiyar Hamas, bayan da aka jinkirta da kusan sa’o’i uku, a lokacin da Firai Ministan Isira’ila Benjamin Netanyahu ya ce ba za’a fara ba har sai Hamas ta bayar da jerin sunayen mutum uku da aka yi garkuwa da su da ake shirin sakin su a yau Lahadi.
Ofishin Netanyahu ya fada a ranar Lahadi cewa, “firai minista ya umarci Rundunar Tsaron Isira’ila ta IDF cewa yarjejeniyar tsagaita wuta da ya kamata ta fara aiki da karfe 8:30 na safe, ba za ta fara aiki ba har sai Isira’ila ta samu jerin sunayen mutanen da aka yi garkuwa da aka saki da Hamas ta yi alkawari za ta bayar.”
Daga karshe dai Hamas ta bayar da sunayen, kuma Isira’ila ta ce za a fara tsagaita wuta da karfe 11:15 na safe.
Hamasa dai ta dora alhakin jinkirin bayar da sunayen ne kan wasu dalilai na fasaha, inda ta kara da cewa, a cikin wata sanarwa da ta fitar, tana mai tabbatar da aniyar ta ga yarjejeniyar tsagaita wuta da aka sanar a makon da ya wuce.
An shirya tsagaita wutar ne za ta fara aiki a safiyar Lahadin nan da misalin karfe 8:30 agogon yankin, mai shiga Tsakani kasar Qatar ta fada ranar Asabar, bayan da majalisar ministocin Isira’ila ta kada kuri’ar amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma sako wadanda aka yi garkuwa da su.
Bayan wani taro da ya dauki sama da sa’ao’i shida da sanyin safiyar ranar Asabar, gwamnatin Isira’ila ta maince da yarjejeniyar da za ta kai ga kawo karshen yaki da kungiyar Hamas da aka shafe watanni 15 ana gwabzawa a Zirin Gaza.
Dandalin Mu Tattauna