Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yara Biyu Sun Hallaka A Wata Gobara Da Ta Tashi A Sansanin 'Yan Gudun Hijra A Borno


Tsohon hoton wani sansanin 'yan gudun hijira da gobara ya lakume
Tsohon hoton wani sansanin 'yan gudun hijira da gobara ya lakume

A yau Talata, wani ibtila'i ya abkawa jihar Borno, inda gobara ta kone sansanin 'yan gudun hijra na Muna dake shiyar Muna na jihar dake yankin arewa maso gabashin Najeriya, wanda yayi sanadiyar mutuwar yara 2.

WASHINGTON DC - Har sa'ilin hada wannan rahoton ba'a kai ga tantance musabbabin tashin gobarar ba.

Kuma, har yanzu gwamnatin Borno ko rundunar 'yan sandan jihar basu ce uffan game da al'amarin ba.

Jihar Borno na fama da masu tada kayar bayan kungiyar Boko Haram tsawon gwamman shekaru al'amarin da yayi sanadiyar asarar dubban rayuka da raba dimbin jama'a da gidajensu.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG