Jami’an kasar Indiya sun gano wata dukiya da aka boye a wani wurin ibada dake kudancin kasar da aka kiyasta kan biliyoyin dala. An gano daimon da duwatsu masu kawa da kudin zinari da azurfa da kuma kananan mutum mutumi a wani akwatin ajiya na karkashin kasa cikin wurin ibadar, inda tsofaffin sarakunan Travancore suke ayyukan ibada, dake jihar Kerala ta kudancin kasar. An tura daruruwan sojoji su yiwa tsohon wurin ibadar kawanya yayinda aka sa na’urar tsaro a kofar shiga wurin ibada, bayanda aka fara yayata rahoton ganon dukiyar jiya asabar. Jami’an kasar Indiya sun yi kiyasin cewa, kudin dukiyar zai kai dala biliyan goma sha daya da miliyan dari biyu.
An gano dukiya ta biliyoyin dala a wani akwatin ajiya na karkashin kasa a wani wurin ibada a kasar Indiya
Jami’an kasar Indiya sun gano wata dukiya da aka boye a wani wurin ibada dake kudancin kasar da aka kiyasta kan biliyoyin dala.