Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tace Amurka, tana goyon bayan shirin Girka na farfado da tattalin arzikin kasar da kuma takalar basusuka da suka yiwa kasar kanta. Clinton ta bayyana a birnin Athens yau Lahadi cewa, Amurka tana goyon bayan yunkurin gwamnatin kasar Girka na yin garambawul da zasu taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasar. Bayan ganawa da ministan harkokin kasashen ketare na kasar Girka Stacros Lambrinidis, Clinton ta bayyana cewa, garambawul kwakkwarar hanya ce ta na farfado da tattalin arzikin kasa ta kuma ce Amurka tana da kwarin guiwa a kan kasar. Lambrinidis ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Girka mai ci yanzu zata ba marar da kunya yayinda kasashen ketare ke ganin kasar zata durkushe. Kasar Girka tana shirin gudanar da taron koli na gaggawa ranar alhamis a birnin Brussels, inda shugabannin kasashe goma sha bakwai zasu yi kokarin cimma matsaya kan kaso na biyu na rancen kudin da aka amince da ba kasar domin farfado da tattalin arzikinta. Gwamnatin kasar Girka karkashin jagorancin PM George Papandreou ta aiwatar da shirin tsuke bakin aljihu da zumar samun karin rance daga kasashen turai da kuma cibiyar kasa da kasa.
Sakatariyar ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta goyi bayan shirin farfado da tattalin arzikin kasar Girka
Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tace Amurka, tana goyon bayan shirin Girka na farfado da tattalin arzikin kasar da kuma takalar basusuka da suka yiwa kasar kanta.