An girmama tsohon ‘dan wasan Chelsea Frank Lampard, a matsayin ‘dan wasan da yafi kowa jefa kwallaye cikin raga a wasannin lig lig na Firimiya, bayan da ya jefawa tsohuwar kungiyarsa Chelsea kwallo a raga lokacin da yake a Manchester a matsayin rance. Wanda ke da irin wannan tarihi kafin Lamparda shine Andy Cole.
A cewar Lampard, “nayi aniyar shiga cikin tarihi a rayuwata, amma ban taba tsammanin wannan dana samu ban taba tsammanin zan taba samun sa ba. ina matukar son littafin tarihi kuma ina karanta shi nida ‘ya ta kafin na kwantar da ita” yaci gaba da cewa ina jin wani iri inna zarga kwallo a raga, amma yanzu sun shigar da ni cikin littafin tarihi, ina matukar farin ciki da ita.
Shima tsohon shugaban sa wato Mourinho, ya sami wasu lambobin yabo har hudu wanda aka bashi shadar shiga littafin kamar haka; shine wanda yafi kowa samun maki a wasannin Firimiya lig (95 point), wanda yafi kowa samun zama zakaran wasan Champion lig a kungiyoyi daban daban, manaja mafi kankantar shekaru da fafata a wasanni ‘dari a Champion Lig, na karshe kulob dinsa shine kulob din daba kasafai ake cinye su a gida ba.
Jose Mourinho mai shekaru 52 da haihuwa yace, “abin dadi anan shine zan iya rataye lambobin kyautar da aka bani a bangon ofishina. Abin jin dadi ne wanda kan yaro baka taba tunanin zai faru da kai ba.
Daga karshe Ronaldo sami lambar yabo ta ‘dan wasan da yafi kowa zarga kwallaye uku-uku a wasannin La Liga, kuma wanda yafi kowa mabiya a shifukan sadarwa na zamani a facebook da twitter yana da mabiya sama da miliyan 27.