Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Super Eagles Ta Sha Alwashin Lallasa Tanzaniya


A wani sako da Kungiyar kwallon kafar Super Eagles ta aikawa Kaftin din ‘yan wasan Vincent Onyeama wanda ke zaman makokin rasa mahaifiyar sa a ‘yan kwanakin da suka gabata, Ahmed Musa ya sha alwashin cewa Super Eagles zata doke Tanzaniya a wasan da zasu buga ranar asabar mai zuwa.

A halin yanzu an ba Musa rukon kwaryar matsayin kaftin din kungiyar ‘yan wasan ne, biyo bayan kasancewar kaftin din kulob din baya nan da kuma rashin Mikel Obi a cikin ‘yan wasan.

Musa ya fada wa mujallara completesportnigeria.com cewar Enyeama zai ci gaba da kasancewa kaftin din tawagar ‘yan wasan har sai lokacin da ya ga damar bari kokuma ajiye aiki.

“dan wasa ne na kwarai, kuma ina bashi girman sa kuma zan kama mashi aikin a Tanzaniya kawai kuma cikin farin ciki zan hanunta masa matsayin sa da zarar ya dawo wurin wasa mai zuwa.

Musa ya kara da cewa “Muna yi masa gaisuwar ta'aziyya, kuma zamu lallasa Tanzaniya domin sa , kumja zamu yi aiki da dukkan karfin mu da kwazon mu domin samun kyakkyawar nasara a wasan da zamu buga a dares Salam.”

Da aka tambaye shi yadda yaji a matsayin mai jagorancin kungiyar CSKA Winger ya maiyar da martanin cewa, farin ciki na Kawai shine mu dake Tanzaniya.

Kungiyar Super Eagles ta Najeriya na cigabab da zama mai matsayi na 53 ada hukumar FIFA ta fitar ranar 3 ga watan Satumbar wannan shekarar.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG