Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Karrama Wani Dan Afrika Da Lambar Yabo Mafi Girma A Duniya


An bada lambar yabo ga wani dan Afrika, a wani yunkuri da yayi na taimakama mata a Demokaradiyyar Congo.

Mutanen biyu da suka lashe lambar yabo akan zaman lafiya ta Duniya na shekara nan 2018, sun hada da Nadia Murad, wata yar fafutika ta Yazid wacce ta sha wahala a hannun 'yan kungiyar ISIS, a Iraq tare da Denis Mukwege wani likita wanda ya kware akan binciken lafiyar mata, wanda assibitin shi dake Jamhuriyar Demokradiyar Congo wada ta kula da mata fiye dubu 50, wadanda suka fuskanci walakanci da kuma tilasta musu yin jima’i ba tare da yardarsu ba.

Kwamitin bada kyautar Nobel na kasar Norway, ya fada a cikin wata sanarwar a ranarJuma’a cewar, wannan kyautar an bada ita ne saboda namijin kokarinsu, wajen ganin an kawo karshen wulakancin tilasata mata jima’i alatilas a matsayin wani makami na yaki.

Mukwege dan shekaru 63 da haifuwa yana gudanar da wata assibiti mai suna Panzi Hospital dake gabashin kasar Demokradiyar Congo, inda 'yan bindiga suke amfani da lamarin fyade domin azabtarda mazaunan yankin.

Likitocin wannan asibiti sun sha taimaka ma mata da dama da suka sami raunuka a lokacin da ake musu fyade a lokacin yakin basasar kasar ta Congo.

A Jiya Juma’a Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya yabawa Dr. Mukwege, wanda ya bayyana a matsayin wani fittacen zakara wajen kare hakkokin mata da aka yiwa fyade.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG