Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Zimbabwe Sun Ceto Yara 251 Da Ake Bautar Da Su A Wata Kungiyar Addinin Kabukabu


Zimbabwe - Addinin Kabukabu
Zimbabwe - Addinin Kabukabu

‘Yan sandan kasar Zimbabwe a ranar Larabar da ta gabata sun ce sun kama wani mutum da ke da’awar cewa shi Annabin mabiya darikar manzanni ne a wani wurin ibada da mabiyansa ke zama a wani waje.

WASHINGTON, D. C. - Haka kuma hukumomi sun gano kaburbura 16 da ba a yi wa rajista ba, ciki har da na jarirai, da kuma yara sama da 250 da ake bautar da su ana amfani da su a ayyuka daban-daban.

Zimbabwe
Zimbabwe

A cikin wata sanarwa da kakakin 'yan sanda Paul Nyathi ya fitar, ya ce Ismael Chokurongerwa, mai shekaru 56, ya yi ikirarin cewa shi Annabi ne kuma ya jagoranci wata kungiyar da ke da mambobi sama da 1,000 a wata gona mai tazarar kilomita 34 daga arewa maso yammacin babban birnin kasar, Harare, inda yaran suke zaune tare da sauran mabiyansa.

Ya ce "ana amfani da yaran don yin wasu ayyukan domin amfanin shugaban ƙungiyar," in ji shi. Daga cikin yara 251, yara 246 a cikin su ba su da takardar shaidar haihuwa.

“‘Yan sanda sun tabbatar da cewa duk yaran da suka kai shekarun zuwa makaranta ba sa zuwa karatun boko kuma ana cin zarafinsu a matsayin aiki mai arha, suna yin ayyukan hannu da sunan koya musu dabarun rayuwa," in ji Nyathi.

Zimbabwe
Zimbabwe

‘Yan sandan sun ce daga cikin kaburburan da suka gano akwai na jarirai bakwai wadanda ba a yi wa rajistar haihuwa ko jana’izar su ba.

Ya ce jami’an ‘yan sanda sun kai samame wurin ibadar a ranar Talata. An kama Chokurongerwa, wanda ya kira kansa Annabi Isma'il, tare da wasu mataimakansa guda bakwai "saboda laifukan da suka hada da cin zarafin kananan yara." Nyathi ya ce za a fitar da ƙarin cikakkun bayanai "a kan lokaci yayin da bincike ke gudana."

Daya daga cikin mataimakan Chokurongerwa ya yi hira da jaridar, y ace

Zimbabwe
Zimbabwe

“Imaninmu ba daga nassi ba ne, mun samo shi kai tsaye daga Allah wanda ya ba mu dokoki kan yadda za mu shiga aljanna. Allah ya haramta karatun boko domin darasin da ake koya a irin wadannan makarantu ya sabawa ka’idarsa,” in ji shi, “Allah ya ce mana ba za a yi ruwan sama ba idan muka tura yaranmu makaranta. Dubi ana fama da fari a can, amma duk da haka muna samun ruwan sama a nan. Muna da baiwar ji ta ruhaniya don mu ji muryar Allah, ”in ji shi.

Ƙungiyoyin manzanni waɗanda ke cusa imani na gargajiya cikin koyarwar Pentikostal sun shahara a ƙasar kudancin Afirka.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG