Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sanda Sun Tsaurara Tsaro A Abuja Gabanin Bukukuwan 1 Ga Watan Oktoba


SP Josephine Adeh
SP Josephine Adeh

Gabanin fara bukukuwan murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kan Najeriya karo na 64, rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayyar Najeriya tace ta tura wadatattun jami’ai da kayan aiki zuwa lungu da sako na garin Abuja.

Sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta fitar a yau Litinin, tace an tura jami’an ne da nufin tabbatar da cewa al’ummar birnin sun gudanar da bukukuwan ranar samun ‘yancin kan ba tare da wata matsala ba.

Sanarwar ta kara da cewar tura jami’an zai hada dana bangaren kula da abubuwa masu fashewa da kayayyakin yaki da tarzoma da kuma wadanda zasu rika sa ido akan kai komom jama’a.

Sanarwar ta kara da cewar za’a kawar da zirga-zirgar ababen hawa daga kan hanyoyin da ake sa ran za’a samu tarurrukan jama’a ciki harda yankunan tsakiyar abuja da dandalin eagle square.

A yayin da ake gudanar da shagulgulan bikin ranar samun ‘yancin kan, ‘yan sanda sun bukaci mazauna abuja su zama masu kula, tare da kai rahoton duk wani motsi da basu yarda dashi ba ta hanyar amfani da layukan wayoyin ‘yan sanda na gaggawa.

FCT: 08032003913, 08028940883, 08061581938, 07057337653

PCB: 09022222352

CRU: 08107314192

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG