Kauyen Yalwan Zangam dake bayan Jami’ar Jos kimanin kilomita biyu ne daga cikin birnin Jos.
Shugaban kungiyar raya al’ummar Anaguta, Sunday Bunu ya ce mutane talatin da daya ne aka kashe a harin, wasu da dama kuma suna asibiti ana masu jinya.
Ya ce basu da adadin wadanda suka ji rauni amma suna da yawa kuma an duba su a asibitin jihar wato Plateau Hospital. Ya kuma kara da cewa mutane na cikin fargaba sannan babu tabbas don rashin tsaro a wurin har yanzu.
Sakamakon wannan harin tarzoma ta sake barkewa a cikin garin Jos dalilin da ya sa yanzo gwamnatin jihar ta ayyana dokar hana yawo na sa'a 24.
Masu ruwa da tsaki a jihar Filato na kan bayyana hanyoyin samar da zaman lafiya mai dorewa a Jihar.
Maimartaba Sarkin Kanem Alhaji Muhammadu Mu'azu Muhammdu ya shawarci gwamnati da taba jami’an tsaro na’urori irin na zamani wanda za su iya tunkarar duk wani rashin tsaro.
“Ita gwamnati ta yi kokarin samo kayan aiki wa jami’an tsaro, don idan suna da kayan aiki babu mai gwadawa su.” In ji Sarki Muhammadu.
Saurari rahoto cikin sauti daga Zainab Babaji: