Rundunar ‘yan sandan jihar Neja a Nigeria ta ce tana gudanar da bincike akan wani dattijo dan kimanin shekara 60 da ake zargi da yiwa wata yarinya ‘yar shekara 8 fyade,
Kakakin ‘yan sandan jihar ASP Wasiu Abiodun, ya ce lamarin ya faru a garin Wushishi mai nisan kimanin kilomita 50 daga Minna babban birnin jihar a ranar Asabar 11 ga wannan wata na Yuli,
Wanda ake zargin mai suna Haruna Lawali ya shedawa Muryar Amurka cewa tabbas lamarin ya faru, amma ya danganta abin da "kaddara da kuma aiki irin na "shedan."
“Shi wanda ya kama mu ya biyo mu ne daga baya, ya hau taga, ina ganinsa sai na ce a’uzubillahi, sai ya ce ai ba ka san da a’uzubillahi ba, yau asirinka ya tonu kuma sai na kai ka wajen ‘yan sanda.” In ji Lawali yayin hirarsa da Muryar Amurka.
Kakakin ‘yan sandan jihar Nejan ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da shi a gaban kotu domin fuskantar hukunci daidai da laifin da ya aikata.
Ya kuma shawarci iyaye da jagororin yara da su rika sanya idanu akan zirga-zirgar yaransu.
Hukumar kula da kare hakkin yara ta jihar Neja ta ce ta damu da kara samun yawan aikata fyade a jihar domin a kusan kullum sai an samu korafin yin fyade sau uku a rana.
A 'yan watannin nan, matsalar yiwa yara maza da mata fyade ta kara ta'azzara musamman ma a arewacin Nigeria inda a wasu lokuta ta kan kai ga su rasa rayukansu.
Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari:
Facebook Forum