Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Kamo Wanda Ya Kashe Diyar Tsohon Mataimakin Gwamnan Ondo


Marigayiya Khadija Oluboyo
Marigayiya Khadija Oluboyo

Rundunar 'yan sanda ta Jihar Ondo ta kama wani mutum Adeyemi Alawo, da ta ke zargi da kashe diyar tsohon mataimakin gwamnan jihar Ondo,Lasisi Oluboyo mai suna Khadija.

Kakakin 'yan sandan jihar Ondo, DSP Femi Joseph Femi ya bayyana cewa Adeyemi Alawo ya shigo hannunsu kuma suna binciken lamarin. Sannan mai yiwuwa kwamishinan 'yan sanda na jihar zai yi wa 'yan jarida bayani gobe a game da abin da ake ciki.

Kakakin ya bayyana cewa, sun kamo Alawo ta bayanan da suka samu kuma sun gano cewa ya turbude Khadija a gidansa da ke Akure bayan da ya kasheta amma da ya gano cewa gawarta na wari, sai ya aiki wani ya samo masa ledan bagi domin zuba gawar.

Bayan 'yan sanda sun kammala bincikensu, za a kai shi kotu domin ya amsa laifin da ya aikata, haka kuma suna bin sahun wasun da ke da hannu a cikin wannan aikin rashin imani.

Saurari rohoton

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:41 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG