Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Jaddada Aniyar Tabbatar Da Tsaro A Lokacin Azumin Watan Ramadan


Babban Sufeton Rundunar 'Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun
Babban Sufeton Rundunar 'Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun

A daidai lokacin da aka fara azumin watan Ramadan, Babban Sufeton 'Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya jaddada aniyar rundunar na samar da ingantaccen tsaro ga kowa a fadin Najeriya.

WASHINGTON DC - Sanarwar da kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar a yau litinin a Abuja, tace Egbetokun ya bada tabbacin ne a yayin da yake mika sakon gaisuwa ga al'ummar Musulmi a yayin da suka tashi da azumin watan Ramadan.

An ruwaito sanarwar na cewa, "a wannan wata mai tsarki, Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ta kudiri aniyar tabbatar da zaman lafiya, tsaro da walwalar al'ummar kasa. Rundunar 'Yan Sanda a matsayinta ta hukuma, ta fahimci mahimmancin mutunta addinai da al'adu da kuma bukatar dabbaka akidun hakuri da fahimtar juna da hadin kai a wannan al'umma mai mabambantan jama'a".

Babban Sufeton 'Yan Sandan, ya bukaci al'ummar musulmi su rungumi halayen tausayi da yawan kyautatawa da yafewa juna da watan ramadan ya siffantu dasu.

Ya kuma bukaci a samu hadin kai da tallafawa juna, da dabbaka samun zaman lafiya da kaunar juna da abota da hadin kai a watan Ramadan dama bayansa.

A yayin da yake kira ga al'umma data rungumi tsarin tsaro a unguwani, Babban Sufeton, sannan ya bukaci 'yan Najeriya su taimakawa kokarin rundunarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a watan Ramadan.

Haka kuma, Babban Sufeton ya bukaci al'ummar Musulmi su ci gajiyar albarkar dake tattare da watan Ramadan sa'annan suyi kokari wajen kyautata rayuwar wasu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG