Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Bukaci Amnesty Ta Janye Kalamunta Kan Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa


Sufeta Janar, Dr. Kayode EGBETOKUN
Sufeta Janar, Dr. Kayode EGBETOKUN

gazawar Amnesty wajen yin biyayya ga wannan umarni zai sabbaba rundunar daukar matakin shari’a domin kare mutuncinta.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF) ta aikewa kungiyar kare hakkin bil adama ta “Amnesty International” da wasikar neman ta gaggauta janye kalamai tare da neman gafararta a bayyane dangane da wani rubutu data wallafa mai taken “zubda jini a watan Agusta: gwamnatin Najeriya ta dauki mummunan mataki akan masu zanga-zangar tsadar rayuwa”.

Sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan najeriyar, ACP Muyiwa Adejobi, ya fitar tace wasikar na dauke da kwanan watan 6 ga watan Janairun 2024.

A cewar NPF rubutun da aka wallafan da ke dauke da dimbin ikrari marasa tushe, ya zargi rundunar da tauye hakkin bil adama, da cin zalin ‘yan sanda tare da amfani da karfi fiye da kima yayin zanga-zangar tsadar rayuwar data gudana a watan Agustan 2024.

Sanarwar ta kara da cewa “bayan nazarin mai zurfi da bincike, rundunar ta yi fatali da zarge-zargen a matsayin marasa tushe, inda ta tabbatar da cewa babu kamshin gaskiya a cikinsu gabadaya kuma basu da makama.

“Amnesty International” ta janye rubutun tare da neman gafararta a bainar jama’a nan da kwanaki 7.”

Ta kara da cewa gazawar Amnesty wajen yin biyayya ga wannan umarni zai sabbaba rundunar daukar matakin shari’a domin kare mutuncinta.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG