Shugaba Jonathan ya bayyana Bafarawa da cewa shi ne tamkar jigo na dukkan ‘yan siyasar jihar Sokoto, wanda ya ga cewa hanya guda ta taimakawa al’ummarsa it ace ta shiga cikin jam’iyyar PDP. Yace samun Bafarawa a cikin jam’iyyar PDP, ya maye gurbin duk masu korafin da suka fice daga jam’iyyar.
Yace Bafarawa da jama’arsa zasu damkawa jam’iyyar PDP nasara a zabubbukan da suke tafe.
Shi ma shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu, ya bayyana Attahiru Bafarawa a zaman amininsa wanda suka fara yin siyasa tare amma a jam’iyyu dabam-dabam. Sai gas hi yau Allah Ya hada su a jam’iyya guda. Yayi masa marhabin da shigowa cikin PDP.
Da yake nasa jawabin, tsohon gwamna Attahiru Bafarawa yaba shugaban kasa tabbacin cewa PDP ba zata ji kunya a Jihar Sokoto ba.