WASHINGTON, DC —
Wasu mata uku, ciki har da kakar 'yar da aka sace, sun fada ragar rundunar 'yan sandan jihar Filato. Kamar yadda wani da ake zargi da kwakule idon wani yaro shi ma ya shiga hannu.
Da yake bayani ma manema labarai a Jos, babban birnin jihar Filato, Kwamishinan 'Yansandan jihar Filato,Chris Olake ya ce 'yan sanda sun yi nasarar bin sawun barayin yarinya 'yar wata takwas da haihuwa har zuwa garin Orka da ke jihar Anambra, inda su ka kwato ta daga hannun wadanda su ka sace ta.
Kwamishinan 'yan sandan ya gaya wa 'yan jirida, ciki har da wakiliyar sashin Hausa Zainab Babaji cewa kakar yarinyar ce ta fara sayar da ita ga Eukeria kan kudi Naira 150,000; ita kuma Eukeria ta sai da ita ma Rita kan kudi Naira 250,000; sannan ita kuma Rita ta sayar ma Grace kan kudi Naira 500,000.
Haka zalika, rundunar 'yansandan ta jihar Filato ta damke wani mutum mai suna Taca-Tali da ake zargi da kwakule idon wani yara mai kiwon shanu.