Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Jam'iyyar APC Mara Rajista Na Barazanar Zuwa Kotu


Shugaban Hukumar Zaben Nijeriya, Furfesa Attahiru Jega.
Shugaban Hukumar Zaben Nijeriya, Furfesa Attahiru Jega.

Jam'iyyar African People Congress (APC, a takaice) mara rajista, na barazanar zuwa kotu.

A Nijeriya, jam'iyyar African People's Congress (APC) ta yi barazanar gurfanar da hukumar zaben Nijeriya saboda kin yin mata rajista. Da ya ke bayani ga wakiliyarmu a Abuja, Madina Dauda, shugaban Jam'iyyar Chief Onyinye Ikeagwuomu ya ce jam'iyyar tasu mai takaitaccen suna "APC" tamkar APC mai rajista wato All Progressive Congress, ta cika sharuddan sashi na 222 na kundin tsarin mulkin Nijeriya da kuma sashi na 78 na dokar zabe. Bugu da kari, ya ce tasu APC din ta riga dayar cika takardun bukatar neman rajista. Don haka, ya ce hukumar zabe ba ta yi masu adalci ba da ta ki yin masu rajista.

To amman da ya ke mai da martani, kakakin hukumar zaben Nijeriya mai zaman kanta Nick Dazang, ya ce an yi wa daya APC din rajista ne sabanin dayar saboda ta cika dukkannin sharuddun samun rajista. Ya ce kafin su yi wa All Progressive Congress (APC) rajista sai da su ka tantance ikirarinta na mallakar ofis da bayyanannar manufa.

Wani jigon jam'iyyar ta All Progressive Congress (APC) kuma gwamnan jihar Kano, Senator Kabiru Gaya ya ce hukumar zaben ta yi gaskiya da ta ce sun cika ka'idar samun rajista. Ya ce ai ita jam'iyyar African People's Congress (APC) na ikirarin ita ta Africa ne ba Nijeriya ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG