Ministar harkokin wajen Ghana Miss Shirley Ayorkor Botchway ta bayana cewar dokar haramtawa baki harakar kasuwancin kayayyakin ba ta shafi yan asalin kasashen kungiyar ECOWAS ba, saboda haka bai shafi ‘yan Nigeria ba. Ministar ta fadi haka ne yayin wata ziyarar ban girma da ta kaiwa takwaran aikinta na Nigeria Mr Geoffrey Onyeama a Abuja.
Wannan maganar cewar baki sun kwace harkokin kasuwancin a Ghana, magana ce da ta samo asali tun lokacin gwamnatin John Dramani Mahama. Gwamnatinsa ce ta haramtawa ‘yan asalin China da Lebanon da Indiya shiga harkokin kasuwanci irin na y au da kullum a kasuwani.
Amma rashin fahimtar ta yanzu ta taso ne a birnin Kumasi cikin jihar Ashanti tsakanin masu sayar da karafan mota, inda su yan asalin Kumasi ke nuna rashin yadda game da yadda ‘yan Nigeria ke ciniki .
Mr Ononso dan Nigeria dake sayar da kayan karafa ya musanta zargin cewa su ‘yan Nigeria na batawa ‘yan Ghanan kasuwanci. Su ‘yan Ghana sun zargi ‘yan Nigeria da sayar musu kaya da tsada. Misali, wai abun dubu dari takwas sai su sayar musu akan miliyan daya. Dalili ke nan da ‘yan Ghana ke cewa ‘yan Nigeria na bata masu harkokin kasuwanci duk da cewa dokarsu ta hana wani bako mallakar shago a kowace kasuwar kasar.
Amma ‘yan Nigeria na cewa idan sun ba ‘yan Ghana kaya su sayar ba sa biyansu bayan sun sayar da kayan dalili ke nan su ma su kan sayar da kansu ko su bayar da tsada.
A saurari rahoton Ridwan Muktar Abbas
Facebook Forum