Shugaban Ghana Nana Akufo Addo ya gabatar da jawabinsa na shekara- shekara kan halin da kasar ke ciki ga Majalisar Dokokin kasar.
Kundun tsarin mulkin kasar ya ba shugaban damar halartar majalisa kowace shekara ya bayyana halin da kasar ke ciki.
A jawabinsa na sa'o'i biyu, shugaban ya tabo duk fannonin rayuwa a kasar tare da sake jaddada aniyar gwamnatinsa na yaki da cin hanci da rashawa.
Ya yi alkawarin kafa ofishi mai daukaka kara na musamman akan cin hanci da rashawa.
Ya kuma yi fatan majalisar za ta hanzarta amince wa da wanda ya gabatar mata.
A fannin tattalin arziki shugaban ya ce ko da yake, ya gaji tulin bashi amma tattalin arzikin kasar ya bunkasa daga kashi 3 zuwa kashi 7.
Saurari rahoton Ridwanullah Abbas Muktar domin jin tsokacin da mutane suka yi kan wannan jawabi na sa.
.
Facebook Forum