Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Ghana Ya Sallami Ministan Makamashin Kasar


Shugaban Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo
Shugaban Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo

Shugaban kasar Ghana Akufo Addo ya yi waje da ministan makamashin kasar Boakye Agyarko kodayake bai bayyana dalilin yin hakan ba amma wasu masana na ganin korar ministan na da nasaba da irin rufa rufar da aka yi a ma'aikatar

Shugaban kasar Ghana ya sallami ministan makamashin kasar, Boakye Agyarko daga mukaminsa.

Duk da cewa bai bayyana dalilin ko dalilan da suka sa ya sallameshi daga aiki ba masu kula da harkokin kasar, suna zargin cewa ministan na da hannu dumu-dumu cikin wata muna-munar da aka yi a harkar man fetur din kasar.

BOAKYE AGYARKO: Ministan Makamashi da aka salama
BOAKYE AGYARKO: Ministan Makamashi da aka salama

Sakataren ma'aikatan man fetur na kasar ya yabawa shugaban kasar inda ya ce hakika shugaba Akufo Addo ya yi adalci da korar ministan. Ya ce tun daga watan Fabrairu suke kira a tsige ministan saboda yin rufa-rufa da sanya hannu a wata yarjejeniyar hakan man fetur da ya cutar da kasar.

A cewar masu ruwa da tsaki a harkar kasar yanzu kam sun tashi ba za su bari a yi masu dodorido ba musamman a harkar man fetur a kasar.

A saurari rahoton Ridwan Abbas da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG