Bankin na CBN ya cimma yarjejeniyar ce bayan zama da hukumar kula da kamfanoninin sadarwa ta Najeriya NCC inda suka tsayar da biyan cajin Naira shida da kwabo casa'in da takwas (6.98) ga duk sakon kudi da mutum ya tura ta wayar salula.
Matakin ya biyo bayan dimbin bashin da ya taru ne kan tsarin aika kudi wato USSD a takaice da ya sanya har kamfanonin sadarwar su ka yi barazanar jingine tsarin.
Karin bayani akan: CBN, NCC, USSD, Nigeria, da Najeriya.
Sabon tsarin da ya fara aiki daga ranar 16 ga wannan watan na Maris ya nuna sau daya za a yi cajin na nera 6.98, maimakon ga duk sakon kudi da mutum zai aika ta wayar salula.
Mai sharhi kan tattalin arziki a Najeriya Yusha'u Aliyu yace cajin kudin ba laifi ba ne amma bai kamata ya wuce kima ba duba da yawan 'yan Najeriya.
Mustapha Aliyu, dan kasuwa da ke zaune a Abuja, ya ce ya kamata gwamnati ta duba lamarin don tattalin arzikin kasa da kasuwanci su bunkasa.
Babban bankin Najeriya tare da hukumar NCC sun cimma bin matakin biyan dukkan bashin da kamfanonin sadarwar ke bi kuma ba za a bar bankuna su karbi karin caji ba bayan wanda aka karba na USSD.
Saurari cikakken rahoton Hauwa Umar a sauti: