Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Saki Pastor Bulus Yikura


Pastor Bulus Yikura.
Pastor Bulus Yikura.

Kungiyar mayakan Boko Haram ta sako Pastor Bulus Yikura, sa’o’i 24 kafin wa’adin da kungiyar ta bayar na kashe shi.

Wani hoton bidiyo ya karade kafafen sada zumunta na internet, wanda ke nuna malamin a gurfane yana neman agaji, inda yake kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya da kungiyar kiristocin kasar, da su kawo dauki domin ceto rayuwarsa da ke cikin hatsari.

Yikura, wanda wani dan kungiyar Boko Haram yake a bayansa rike da wuka a hoton, ya bayyana cewa an ba shi wa’adin “kwana bakwai” da zai kare a yau Alhamis, domin ya nemi taimakon da zai fitar da shi daga halin da yake ciki.

Pastor Bulus Yikura
Pastor Bulus Yikura

“Idan har da gaske kuna son ceto rayuwa ta daga halin da nake ciki, to kuwa ya zama wajibi ku hanzarta yin wani abu cikin gaggawa”, in ji Pastor Yikura a cikin hoton bidiyon.

Mayakan Boko Haram sun kama Partor Yikura a ranar jajibirin kirsimetin da ya gabata, sa’adda suka kai hari a garin Pemi da ke cikin karamar hukumar mulkin Chibok ta jihar Borno, kuma tun a lokacin yake hannun ‘yan kungiyar.

A ranar 24 ga watan Fabrairu kuma shugaban Boko Haram Abubakar Shekau, ya ba da wa’adin kwanaki 7 wanda zai kare a ranar Alhamis, ga gwamnatin Najeriya da ta yi wani abu domin sakin malamin na majami’a.

Nigeria Boko Haram
Nigeria Boko Haram

To sai dai ba’a bayyana taka-maiman bukatar da kungiyar ta Boko Haram ta gabatar ba domin sakin Yikura.

A ranar Talatar da ta gabata kuma majalisar Wakilan Najeriya ta tattauna lamarin a zamanta na ranar, inda ta bayyana damuwa akan rashin ceto paston, a yayin da wa’adin da aka bayar na kashe shi ke neman karewa.

A kan haka majalisar wakilan ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar matakin ganin an ceto rayuwarsa.

An ga Pastor Bulus Yikura wanda ya sami ganawa da iyalansa bayan sako shi a Maiduguri, tare da rakiyar wasu jami’an tsaro.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton kuma, babu bayani akan yanayin matakin da aka dauka na ceto malamin na addinin kirista.

XS
SM
MD
LG