Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da ‘Yan Najeriya 190 Gida Daga Hadaddiyar Daular Larabawa


Jirgin saman Emirates
Jirgin saman Emirates

Gwamnatin tarayyar ta kwaso jumlar ‘yan Najeriya 190 da suka makale a Hadaddiyar Daular Larabawa zuwa gida.

A cewar sanarwar da Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta fitar mai dauke da sa hannun babban daraktanta mai kula da shiyar arewa ta tsakiya, Bashir Garga, a yau Talata, tace ayarin jami’an gwamnati karkashin jagorancin NEMA sun tarbi mutanen da suka dawo gidan a filin saukar jiragen saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja da misalin karfe 5 da mintuna 57 na asubah.

NEMA ta kara da cewar hukumomin daya kamata sun dauki bayanan mutanen, tare da jan hankalinsu akan “zama mutane na gari” bayan da suka dawo Najeriya.

“Gwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan Najeriya, su zamo jakadun kasar nan na gari, tare da dabbaka akidun kishin kasa da bin doka da oda da zama sahihan mutane masu mutunci.”

Idan za’a tuna, a watan Oktoban 2022, gwamnatin tarayya ta dawo da jumlar mutane 542 gida daga Hadaddiyar Daular Larabawa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG