Kwanaki tara bayan yunkurin hallaka Trump, lamarin da ya girgiza al'ummar kasar, an samu amsoshi kan yadda mai harbin ya samu kusanci da Trump.
A karon farko Shugabar Hukumar tsaron farin kaya Amurka Kimberly Cheatle, ta amsa tambayoyin 'yan majalisar game da harbin, inda tace, "hakika Mun gaza."
Cheatle ta ce za a fitar da cikakken rahoton hukumar a cikin kwanaki 90. Sai dai ‘Yan majalisar sun ce hakan bai dace ba, sabili da a lokucin zabe ne, zaben da ke cike da rudani. Wasunsu sun kira ta da ta yi murabus.
Dan Majalisa na Jam’iyyar Republican James Comer, ya bayyana cewa, “Hukumar ta gaza gudanar da aikin ta, bata yi abinda ya dace ba a ranar 13 ga watan Yuli, da kuma kwanaki kafin gudanar da taron. Ma'aikatar tana da dubban ma'aikata da kuma kasafin kudi mai mahimmancin gaske, amma ta gaza yin aikin ta."
Sauraron zaman na ranar Litinin dai shi ne na farko a kokarin da Majalisar Dokokin kasar ke yi na na gano yadda hukumar leken asirin ta kasa hana yunkurin kashe tsohon shugaba Trump.
Cheatle ta shaidawa ‘yan Majalisar cewa, ma'aikatar leken asirin ce ke da alhakin kare Shugaba Joe Biden, Trump, da wasu mutane 34, da kuma wasu manyan jami’an kasashen waje da suka ka wo ziyara Amurka.
Hukumar tana da ma'aikata kusan 8,000 da suka hada da jami'ai masu sanye da kayan aiki da wakilai na musamman. Cheatle ta bayyana cewa, ana da burin daukar wasu ma’aikata 1,000 "domin biyan bukatun gaba da kuma duk wata bukata da za ta taso."
A ranar Laraba ne dai daraktan hukumar ta FBI da ke gudanar da nata bincike kan yunkurin kisan gillar, zai gurfana a gaban kwamitin shari'a na Majalisar.
Jami'an tsaron kasar Amurka da jami'an tsaro sun kwashe shekaru suna gargadin cewa, kasar na fuskantar karin barazanar tsaro.
Binciken da aka gudanar kan zamantakewar al’umma na nuni da cewa, babbar barazanar ta na zuwa ne daga daidaikun mutane ko kuma kananan kungiyoyi, wadanda galibi ke haushi a kan wani abu.
Bincike na baya-bayan nan kan rayuwar al’umma da aka fitar a watan Satumban da ya gabata, ya kuma yi gargadin cewa, za a iya kai hare-hare kan "jami'an gwamnati, masu jefa kuri'a, da ma'aikatan zabe da kayayyakin more rayuwa, gami da wuraren zabe, wuraren jefa kuri'a, wuraren rajistar masu zabe, abubuwan yakin neman zabe, jam'iyyun siyasa. ofisoshi, da wuraren kirga kuri'u."
Dandalin Mu Tattauna